logo

HAUSA

Habasha ta karbi kashin farko na rigakafin COVID-19 miliyan 2.2 daga shirin COVAX

2021-03-08 09:43:14 CRI

Kasar Habasha ta karbi kashin farko na rigakafin COVID-19 miliyan 2.2 daga shirin nan na COVAX, wanda ke da muhimmanci ga yakin da kasar ta gabashin Afrikan ke yi na dakile ci gaba da yaduwar cutar.

An karbi alluran rigakafi miliyan 2.2 ne a jiya, yayin wani biki da ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin kasar da wakilan ofisoshin diflomasiyya da na MDD dake kasar.

Zuwa safiyar jiyan, mutane 165,029 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da ta yi sanadin mutuwar mutane 2,420 a kasar.

Daraktan cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, John Nkengasong, ya ce samar da rigakafin COVID-19 ga kasashen Afrika, ya nuna kokarin tabbatar da kiwon lafiya da adalci.

Zuwa jiya Lahadi, alkaluman cibiyar Afrika CDC sun nuna cewa, mutane 3,955,148 ne suka kamu da cutar, inda 105,490 suka mutu sanadiyyarta a fadin nahiyar. (Fa’iza Mustapha)