logo

HAUSA

WHO ta jinjinawa fara gudanar da rigakafin COVID-19 a kasashen Afirka

2021-03-12 09:52:52 CRI

Daraktan shiyyar Afirka a hukumar lafiya ta duniya WHO Mr. Matshidiso Moeti, ya ce aikin rigakafin COVID-19 na gudana yadda ya kamata a sassan nahiyar Afirka, duba da yadda tuni adadin wadanda suka karbi rigakafin cutar ya kusa miliyan 4.

Matshidiso Moeti, wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Alhamis, cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce isar karin alluran rigakafi nahiyar, zai karfafa tasirin dakile yaduwar wannan annoba.

Sai dai kuma a cewar jami’in, a yanzu, ma’aikatan lafiya dake kan gaba wajen tunkarar cutar, da sauran mutane masu yanayi na musamman ne ake baiwa muhimmanci, wajen karbar rigakafin cutar ta COVID-19. Nairobi.

A cewar hukumar WHO, kasashen nahiyar Afirka 22, sun riga sun karbi sama da alluran rigakafin COVID-19 miliyan 14.6, tun daga ranar 24 ga watan Febrairun da ya gabata, karkashin shirin nan na COVAX. (Saminu)

Saminu