logo

HAUSA

Ziyarar malam Aliyu Abubakar a Beijing(A)

2020-10-20 19:48:58 CRI

Ziyarar malam Aliyu Abubakar a Beijing(A)

Aliyu Abubakar, jami'in hulda da jama'a ne dake aiki a babban kamfanin man fetur na Najeriya, wato NNPC. A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, malam Aliyu Abubakar ya bayyana yadda ziyararsa a kasar Sin ta kasance, wato lokacin da ya zo halartar taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma FOCAC a takaice a shekara ta 2018 a birnin Beijing.

Malam Aliyu Abubakar ya ce ya ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, kuma ya taba ziyartar wasu wurare masu ban sha'awa a Beijing, ciki har da babbar ganuwa wato Great Wall. Game da taron FOCAC kuma, Aliyu Abubakar ya ce, taro ne mai amfani kwarai da gaske, musamman wajen inganta hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Haka kuma ya bayyana wasu daga cikin kusoshin gwamnati a tawagar Najeriya da suka halarci taron a wancan karo.(Murtala Zhang)