![]() |
|
2020-10-20 19:48:57 cri |
Malam Aliyu Abubakar ya ce ya ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, kuma ya taba ziyartar wasu wurare masu ban sha'awa a Beijing, ciki har da babbar ganuwa wato Great Wall. Game da taron FOCAC kuma, Aliyu Abubakar ya ce, taro ne mai amfani kwarai da gaske, musamman wajen inganta hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Haka kuma ya bayyana wasu daga cikin kusoshin gwamnati a tawagar Najeriya da suka halarci taron a wancan karo.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China