Kabiru Bashiru: Fatana shi ne Najeriya da Sin za su inganta hadin-gwiwa a fannin gina tashoshin jiragen ruwa
2020-05-26 13:19:06 CRI
A cikin shirinmu na wannan mako, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da wani dalibi dan jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a fannin kimiyya da fasaha ta harkar sufurin jiragen ruwa a jami'ar Ningbo ta lardin Zhejiang. A zantawar tasu, malam Kabiru Bashiru ya bayyana ra'ayinsa game da bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da Sin, da yadda yake jin dadin karatu da rayuwa a kasar. Sa'annan ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi ya karanta ilimin da ya shafi sufurin jiragen ruwa a kasar Sin, musamman a matsayinsa na dan arewacin Najeriya.
Har wa yau, Kabiru Bashiru ya yi tsokaci kan irin ci gaban da kasar Sin ta samu, musamman a fannin gina manyan tashoshin jiragen ruwa, da yadda take gudanar da ayyukan surufin jiragen ruwa. Haka kuma ya yabawa matakan da gwamnatin kasar ta dauka a fannin kandagarkin annobar numfashi ta COVID-19. (Murtala Zhang)