2020-05-26 13:19:05 cri |
A zantawar tasu, malam Kabiru Bashiru ya bayyana ra'ayinsa game da bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da Sin, da yadda yake jin dadin karatu da rayuwa a kasar. Sa'annan ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi ya karanta ilimin da ya shafi sufurin jiragen ruwa a kasar Sin, musamman a matsayinsa na dan arewacin Najeriya.
Har wa yau, Kabiru Bashiru ya yi tsokaci kan irin ci gaban da kasar Sin ta samu, musamman a fannin gina manyan tashoshin jiragen ruwa, da yadda take gudanar da ayyukan surufin jiragen ruwa. Haka kuma ya yabawa matakan da gwamnatin kasar ta dauka a fannin kandagarkin annobar numfashi ta COVID-19. (Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China