logo

HAUSA

Kande Ma: Karo ilmi a Najeriya ya sa na kara fahimtar kasar

2020-04-14 15:11:39 CRI

 

 


A kwanan baya, wakiliyarmu Kande Gao ta samu damar yin hira tare da Basiniya da ke koyon harshen Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Tianjin da ke kasar Sin. Sunanta na Hausa shi ne Kande, kuma a shekarar bara, ta samu damar karo ilmi a Jami'ar Bayero. A cikin hirar, dalibar Kande ta bayyana yadda ta ji dadin karatu da zama a Kano, da ma yadda take karatu a gida bayan dawowarki daga Najeriya sakamakon bullowar cutar COVID-19 a Sin.