logo

HAUSA

Masanin tattalin arziki Bello Ado: Kasar Sin za ta taimaka sosai ga farfadowar tattalin arzikin duniya bayan cutar COVID-19 <?xml:namespace prefix = o ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />

2020-04-01 11:02:05 CRI

Masanin tattalin arziki Bello Ado: Kasar Sin za ta taimaka sosai ga farfadowar tattalin arzikin duniya bayan cutar COVID-19 <?xml:namespace prefix = o ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />

A shirinmu na wannan mako, wakilinmu Murtala Zhang ya tattauna da shehun malami Bello Ado, malami a sashen koyar da tattalin arziki na jami'ar BUK, wato Bayero University dake jihar Kano a tarayyar Najeriya.

A zantawar tasu, malam Bello Ado ya bayyana cewa, cutar COVID-19 dake addabar duniya, na yin illa sosai ga tattalin arziki, gami da harkokin kasuwancin duniya, kuma ya kamata gwamnatocin kasashe daban-daban su dauki matakan da suka dace domin rage illar da take haifarwa, ciki har da gwamnatin Najeriya. Bello Ado ya kara da cewa, a halin yanzu cutar COVID-19 na yin sauki sosai a kasar Sin, kuma farfadowar tattalin arzikin kasar na da alaka sosai da farfadowar tattalin arzikin duk duniya.(Murtala Zhang)