Maryam Yahaya Baban Yaya
2019-08-14 15:51:42 CRI
Masu sauraro, yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata bakuwa daga tarayyar Najeriya, wato Maryam Yahaya Baban Yaya, wadda ke karatun ilmin likitanci a birnin Jinzhou da ke arewa maso gabashin kasar Sin.
A cikin zantawar da wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta yi da ita, Maryam Yahaya Baban Yaya ta yi bayani kan yadda take karatu da zama a nan kasar Sin, da ma yadda ci gaban kasar Sin ya burge ta sosai. Bugu da kari kuma, a matsayinta ta mace, a cikin wannan shirin namu na "In ba ku ba gida", Hajiya ta yi tsokaci kan muhimmancin samun ilmi, musamman ma ga mata. A ganinta ilmi jigo ne na rayuwa, don haka Maryam ta yi kira ga mata da su tashi su samu ilmi kada su nemi dogaro kan saura. (Kande Gao)