Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Maryam Yahaya Baban Yaya
2019-08-14 15:51:41        cri

Masu sauraro, yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata bakuwa daga tarayyar Najeriya, wato Maryam Yahaya Baban Yaya, wadda ke karatun ilmin likitanci a birnin Jinzhou da ke arewa maso gabashin kasar Sin.

A cikin zantawar da wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta yi da ita, Maryam Yahaya Baban Yaya ta yi bayani kan yadda take karatu da zama a nan kasar Sin, da ma yadda ci gaban kasar Sin ya burge ta sosai. Bugu da kari kuma, a matsayinta ta mace, a cikin wannan shirin namu na "In ba ku ba gida", Hajiya ta yi tsokaci kan muhimmancin samun ilmi, musamman ma ga mata. A ganinta ilmi jigo ne na rayuwa, don haka Maryam ta yi kira ga mata da su tashi su samu ilmi kada su nemi dogaro kan saura. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China