logo

HAUSA

Najeriya ta nada sabon daraktan tsare tsaren kwallon rugby

2019-05-16 14:03:32 CRI

Hukumar wasan kwallon rugby ta Najeriya (NRFF) ta sanar da nada Abubakar Yakubu a matsayin sabon daraktan tsaren tsarenta. Matakin ya biyo bayan burin da hukumar keda shi ne na bunaksa harkar wasan kwallon rugby a Najeriyar, inji Kelechi Mbagwu, shugaban hukumar ta NRF. Mbagwu ya bayyana Yakubu da cewa mutum ne mai kwarewar aiki a matsayinsa na tsohon dan wasa ana sa ran zai kawo gagarumin sauyi a fagen wasannin kwallon rugby a kasar, ya kara da cewa burinsa shine ganin Najeriya ta shigar da matasa masu yawan a fannin kwallon rugby.

Yace hukumar a shirye take ta mara baya ga duk wani mataki da zai kara bunaksa fannin wasanni a dukkan matakai.(Ahmad Fagam)