Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta nada sabon daraktan tsare tsaren kwallon rugby
2019-05-16 14:03:31        cri
Hukumar wasan kwallon rugby ta Najeriya (NRFF) ta sanar da nada Abubakar Yakubu a matsayin sabon daraktan tsaren tsarenta.

Matakin ya biyo bayan burin da hukumar keda shi ne na bunaksa harkar wasan kwallon rugby a Najeriyar, inji Kelechi Mbagwu, shugaban hukumar ta NRF.

Mbagwu ya bayyana Yakubu da cewa mutum ne mai kwarewar aiki a matsayinsa na tsohon dan wasa ana sa ran zai kawo gagarumin sauyi a fagen wasannin kwallon rugby a kasar, ya kara da cewa burinsa shine ganin Najeriya ta shigar da matasa masu yawan a fannin kwallon rugby.

Yace hukumar a shirye take ta mara baya ga duk wani mataki da zai kara bunaksa fannin wasanni a dukkan matakai.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China