Shugaba Xi ya jaddada cewa, Habasha muhimmiyar aminiyar hadin-gwiwa ce ta kasar Sin a Afirka. Sin na fatan yin amfani da damammakin da suka shafi raya ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya" da sakamakon da aka cimma a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, domin zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni a tsakaninsu.
Abiy Ahmed ya ce, Sin ta dade tana mutunta kasashen Afirka, sannan ba ta tilastawa kasashen Afirka don su yi wani abun da ba su so. Kasashen Afirka sun kuma yarda da karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasa da kasa ta fuskar shawarar "ziri daya da hanya daya", suna kuma nuna cikakken goyon-baya ga raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya. (Murtala Zhang)