Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana game da batun wasikar martani da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikewa wasu daliban makarantar sakandaren Amurka, yayin taron ganawa da manema labaran da aka kira yau, inda ya ce, wannan ba shi ne karo na farko da shugaba Xi ya yi hakan ba, lamarin ya kuma nuna cewa, Xi yana mai da hankali matuka kan cudanya, da hadin gwiwa a bangaren al'adu tsakanin kasa da kasa.
Kwanan baya daliban wata makarantar sakandare dake North Niles ta jihar Illinois ta Amurka, sun rubuta wata wasika da Sinanci ga shugaba Xi, daga baya Xi shi ma ya tura musu wata wasikar da ya rubuta domin ba su amsa, inda ya sa rai cewa, za su kara himmantu kan karatun Sinanci, ta yadda za su taka rawa kan zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin Sin da Amurka, kana ya bayyana cewa, yana fatan za su samu damar zuwa nan kasar Sin domin kara fahimtarsu kan kasar Sin.(Jamila)