Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci atisayen sojojin ruwa na kasashe daban daban, wadanda suka hallara a rawayen teku dake birnin Qingdao na kasar Sin a Talatar nan, a wani bangare na murnar cika shekaru 70, da kafuwar rundunar sojojin ruwa ta 'yantar da al'ummar Sin ko PLA a takaice.
Manyan jiragen ruwa da dama ne dauke da tutocin kasashe daban daban, suka halarci atisayen da dakarun kasashen duniya masu yawa suka gudanar, yayin da kuma wasu jiragen yaki na sama suka rika shawagi a sararin samaniya, cikin yanayi mai matukar ban sha'awa.
A tisayen farko, manyan jiragen ruwan Sin 32 sun yi jerin gwano tare da jiragen yaki na sama 39, ciki hadda jirgin ruwan dakon jiragen yaki na Sin mai suna Liaoning, da kuma jirigin ruwa dake nutso cikin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya. A zango na biyu kuwa, jiragen ruwa 18 daga kasashe 13 sun yi jerin gwano, ciki hadda jiragen kasashen Rasha da na Australia.(Saminu)