Xi ya ce, shawarar "ziri da hanya daya" ta samo asali ne a kasar Sin, amma alherinta ya shafi duniya ne baki daya. Yanzu, shawarar ta zama wani babban dandalin hadin-gwiwar kasa da kasa wadda ke samun karbuwa sosai daga kasashe da dama. Shi wannan kwamitin da aka kafa zai taimako matuka ga raya ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya". Kana, inganta mu'amala da hadin-gwiwa tsakanin kwararrun kasashe daban-daban zai kara samar da fahimtar juna don raya wannan shawara tare.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kafa kwamitin hadin-gwiwar kwararrun kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" zai samar wa kwararrun wani muhimmin dandali na yin tattaunawa da yanke shawara. Xi yana kuma fatan membobin kwamitin za su zurfafa cudanya tsakaninsu, da bada gudummawa ga kara aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" gami da raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.(Murtala Zhang)