Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta samo asali ne a kasar Sin, amma damammakin dake tatattare da shawarar da nasarorin da aka cimma karkashinta dukkansu na jama'ar duniya ne. A cewar shugaban kasar Sin, yanzu haka bangarorin da suka halarci shawarar sun rungumi "ruhun hanyar Siliki" na zaman lafiya da hadin gwiwa, da bude kofa, da hakuri da juna, da koyon fasahohi na juna, da neman amfanawa juna, da cin moriya tare, a kokarin neman mayar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" zama wata shawara mai samar da zaman lafiya, da walwala, da bude kofa, da kyautatuwar muhalli, da sabbin fasahohi, da kuma ci gaban al'adu.
Shugaban ya jaddada cewa, kafofin watsa labaru sun taka muhimmiyar rawa a kokarin musayar ra'ayi tsakanin abokan hadin gwiwar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Yayin da kawancen hadin gwiwar kafofin watsa labarun ya samar da wani dandali na musayar ra'ayi da hadin kai ga kafofin watsa labaru na kasashe daban daban. Shugaba Xi ya ce yana fatan ganin mambobin majalisar kawancen, za su kara yin musayar ra'ayi da hadin kai, don samar da wani yanayi mai kyau na gina shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", ta yadda shawarar za ta baiwa jama'ar kasashe daban daban damar kara amfana da ita. (Bello Wang)