Shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin tsakiya na aikin soja na kasar, Xi Jinping, ya gana da shugabannin tawagogin kasashen waje dake halartar bikin murnar cika shekaru 70 da kafa rundunar sojojin ruwan 'yantar da jama'ar kasar Sin, a yau Talata a birnin Qingdao dake gabashin kasar Sin, inda shugaban ya marabci hafsoshi da sojojin kasashe daban daban da suka zo kasar Sin don halartar wannan biki.
A cewar shugaba Xi, teku yana da muhimmiyar ma'ana ga rayuwar dan Adam da burinsa na neman ci gaba. Sa'an nan yadda za a kiyaye zaman lafiya a yankunan teku ya shafi tsaron kasashe daban daban da moriyar su, wanda ke bukatar damawa da kowa a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Sinawa, a cewar shugaban, mutane ne masu son zaman lafiya, don haka za su tsaya kan turbarsu ta neman ci gaba tare da tabbatar da zaman lafiya. (Bello Wang)