Shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a shekarar 2013, shiri ne da kasar Sin ta gabatar bisa buri guda daya da al'ummomin kasa da kasa ke da shi na samar da wadata ga duniya baki daya.
Ya zuwa yanzu kasashe 126 da kungiyoyin kasa da kasa 29 sun sa hannu kan takardun yin hadin gwiwa dangane da shawarar.
A shekarar 2018 da ta gabata, shugaba Xi ya jaddada bukatar kara azama don kyautata aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".
Nan da wasu kwanaki masu zuwa, za a bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar karo na 2 a nan Beijing, inda shugabanni daga kasashe 37 za su halarta. Yanzu haka an shiga sabon matakai a hadin gwiwar da ake game da aiwatar da shawarar ta "ziri daya da hanya daya". (Tasallah Yuan)