Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin aiwatar da rage haraji a sassan daban daban, don cimma burin samar da kyakkyawan yanayi ga farfadowar kasuwanni.
Mr. Li, wanda memba ne a zaunannen kwamitin koli na hukumar harkokin siyasa ta JSK, ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki, lokacin da yake ziyarar gani da ido a ma'aikatar kudi, da kuma sashen lura da harkokin haraji na kasa.
Ya ce rage haraji da sauran kudaden da ake karba, zai amfani kasar cikin gajere da dogon zango, duba da cewa matakin zai ragewa kamfanoni nauyi, ya kuma taimaka wajen daidaita batun samar da ayyukan yi, baya ga bunkasa tattalin arzikin, da rarraba ribar da kasar ke samu ga dukkanin sassa. Kana hakan zai inganta tsarin kashe kudade na gwamnati.
Firaministan kasar Sin ya kuma ce rage haraji zai kara bunkasa ci gaban kamfanoni, matakin da zai kuma tafiyar da tattalin arzikin kasar Sin bisa turba ta gari, ya kuma bunkasa ci gaban kasar yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)