Yawan tafiye-tafiyen zuwa dazuka ya karu zuwa biliyan 1.6 a shekarar da ta gabata, kamar yadda bayanan hukumar kula da gandun daji ta kasar Sin ta ayyana.
A bara, kasar Sin ta samar da wasu sabbin hanyoyi 10 a dazukan kasar, wanda shi ne kashin farko na irin wadannan hanyoyi.
Hukumar kula da filaye da gandun dajin kasar Sin ta fitar da wasu ka'idoji wadanda za su kyautata yanayin gandun daji, da nufin bunakasa al'amurran da suka shafi gandun dajin don ci gaban fannin yawon bude ido da kyautata yanayin muhallin halittu. (Ahmad Fagam)