Babban ofishin kwamitin tsakiya na JKS da babban ofishin gudanarwar kasar ne suka fitar da jadawalin.
A cewar daftarin, ya kamata a dauki dabarun tafiyar da harkokin kudi da na ba da rance daban-daban, sannan a karfafawa cibiyoyin hada-hadar kudi gwiwar bada karin rance ga kamfanoni masu zaman kansu da kanana da matsakaitan kasuwanci.
Daftarin ya bayyana cewa, idan suka cimma wasu ka'idoji, kamfanoni masu zaman kansu za su iya fadada hanyar samun rance kai tsaye, sannan za a mara masu baya wajen bayar da takardun lamuni. Har ila yau, ya ce ya kamata cibiyoyin hada-hadar kudi su sanya jari cikin takardun lamunin da kamfanoni masu zaman kansu suka bayar. (Fa'iza Mustapha)