Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Albert Keidel, wanda mamba ne na cibiyar binciken harkokin kasa da kasa ta Amurka wato Atlantic Council, ya ce tattalin arzikin zai ci gaba da samun tagomashi, inda zai tashi daga makin tsakiya da yake kai, zuwa maki mai girma.
Ya kuma alakanta kyakkyawan hasashensa ne da juriyar tattalin arzikin kasar Sin da kuma dabarun kasar na samun ci gaba.
Duk da yanayi mai sarkakiya a wajen kasar, tattalin arzikinta a karshen 2018 na tsaye da kafarsa, wanda ke jaddada samun ingantaciyyar ci gaba.
Bayanai daga hukumar kididdiga ta kasar Sin sun nuna cewa, kasar mafi karfin tattalin arziki na biyu a duniya, ta samu ci gaba da kaso 6.6, wanda ya kai yuan triliyan 90.0309, kwatankwacin dala triliyan 13.28 a 2018, adadin da ya zarce wanda aka yi hasashe na kaso 6.5. (Fa'iza Mustapha)