Yawan tallace-tallace ta shafukan intanet ta hanyar wayoyin hannu ya kai kashi 70 bisa, kuma ana sa ran zai sake karuwa a nan gaba, in ji rahoton, wanda cibiyar yada bayanan kafofin intanet ta kasar Sin ta fitar.
Maudu'in In-feed ads, wanda masu ta'ammali da wayoyin hannu ke iya budewa don shiga shafin tallata ta intanet domin yin sayayya na daga cikin muhimman hanyoyin da kanfanoni ke tallata hajojinsu cikin sauri, wanda ke ci gaba da samun karbuwa a tsakanin al'umma a fagen hada hadar kasuwanci.
Kudaden shiga daga bangaren masu tallata kayayyaki ta hanyar amfani da gajerun fayafayen bidiyo ya samu gagarumin ci gaba a shekarar 2018, inda darajar dandalin ta kara yin kima, ta bangaren yin talla, da kuma kara samun karbuwa, in ji rahoton. (Ahmad Fagam)