Kwamitin aiwatar da gyare-gyare da raya kasar Sin, ya kaddamar da wasu takardun ba da jagora, inda ya bukaci a gaggauta raya yankunan birane zuwa na zamani.
Yankin birane, wani yanki ne da ake mayar da manyan birane masu girma sosai ko kuma manyan biranen da suke kara azama kan bunkasuwar wurare masu makwabta, matsayin cibiyar yankin da suke, sa'an nan za a iya zuwa aiki da kuma komawa gida cikin awa guda.
Kwamitin yana ganin cewa, a shekarun baya, yankunan birane suna samun saurin ci gaba, amma ba a samu kyautatuwar dinkewar sufuri a tsakanin biranen ba, haka kuma biranen ba su taimaka wa juna sosai ba, kana ba a kyautata tsarin raya birane yadda ya kamata ba.
Yayin da kwamitin ya ambato manyan ayyukan sufuri da ke yankunan birane, ya bayyana cewa, za a sa kaimi kan hukumomin wurare da su ba da gata ga motocin dake zirga-zirga sau da yawa kan tagwayen hanyoyi, da gaggauta yayyata amfani da katin ETC mai biyan kudin hanya ba tare da tsayawa ba, da kara azama kan soke tashoshin karbar kudin hanya a tsakanin larduna, da kyautata yadda ake zuwa aiki da dawowa gida kan tagwayen hanyoyi a yankunan birane. (Tasallah Yuan)