Ya ce, a bana, za a karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa a sabbin fannoni, wadanda suka hada da fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama, da yanar gizo ta masana'antu, da kuma fasahar intanet ta 5G mai amfanawa harkokin kasuwanci. A sa'i daya kuma, za a karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa a birane da karkara, da ayyukan sufurin kayayyaki, da kawar da talauci, da kuma raya makamashi da dai sauransu. Bugu da kari, ya ce, za a ba da karin tallafi ga al'umma, musamman ma a fannonin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kuma kiyaye tsofaffi da sauransu.
Kana, za a dukufa wajen kare muhalli, da karfafa ayyukan yin rigakafi kan bala'u. Haka kuma, za a inganta fasahohin kirkire-kirkire, yayin da kuma ake sabunta na'urorin da ake amfani da su. (Maryam)