in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bude sabbin hanyoyin mota na kilomita dubu 86 a bana
2018-12-27 11:12:14 cri
Bisa labarin da aka samu daga taron aikin zirga-zirga na kasar Sin a jiya Laraba, an ce, a shekarar 2018, an gaggauta ayyukan gina ababen more rayuwa a fannin zirga-zirga, inda aka zuba jari na RMB biliyan 792 kan ayyukan gina layukan dogo, da kuma zuba jari na RMB biliyan dubu 2 da dari 3 kan ayyukan gina hanyoyin mota da na ruwa, yayin da aka zuba jari na RMB biliyan 81 kan ayyukan jiragen sama masu amfanawa jama'a.

Kuma bisa hasashen da aka yi, an ce, tsawon layukan dogo da aka gina a bana zai kai kilomita dubu 4, ciki har da layukan dogon jiragen kasa masu saurin gaske na kilomita dubu 2 da dari 6. Sa'an nan, tsawon sabbin hanyoyin mota da aka gina zai kai kilomita dubu 86, ciki har da manyan hanyoyin mota na kilomita dubu 6, da kuma manyan hanyoyin mota na ma'aunin kasa da na ma'aunin jihohi da aka gyara na kilomita dubu 20. Haka zalika kuma, sabbin hanyoyin jiragen ruwan koguna da aka kafa sun kai kilomita dari 7, an kuma gina wuraren saukar da jiragen ruwa na matsayin ton dubu 10 guda 46.

A sa'i daya kuma, an rage kudin da aka kashe a fannin zirga-zirga sakamakon gyare-gyaren da aka yi kan tsarin zirga-zirga. Ya zuwa karshen watan Nubamba, gaba daya an rage kudaden da aka kashe kan wannan aiki kimanin biliyan 88.4, adadin da ya wuce burin da aka tsara na bana. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China