Karfin sana'ar hakkin mawallafi na Sin ya karu da kashi 42 cikin shekaru 5
Kwanan baya, cibiyar nazarin harkokin watsa labarai da wallafa littattafai ta kasar Sin ta fidda rahoton "gudummawar tattalin arziki da sana'ar hakkin mawallafi ta Sin ta bayar a shekarar 2017", inda ta bayyana cewa, daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2017, adadin karuwar darajar sana'ar hakkin mawallafi ya karu daga kimanin RMB biliyan dubu 4 zuwa sama da RMB biliyan dubu 6, wanda ya kai kashi 42%. Musamman a fannonin fasahohin sadarwa na zamani, wasanni kan yanar gizo, da kuma shafuka da hotunan bidiyon intanet da dai sauransu, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin kasar Sin mai inganci. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku