"A kan dauki dogon lokaci game da tsare tsaren da za su raya tattalin arzikin kasar Sin bayan aiwatar da manufofin," Sheng Songcheng na 把babban bankin na kasar Sin (PBOC), shi ne ya bayyana hakan a cikin wasu kalamai da ya furka game da tattalin arziki.
Sheng ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar zai samu daidaituwa ne bayan rukunin watannin ukun farko na shekarar 2019 kana ana sa ran zai daga sama a rukuni na biyu na tsakiyar shekarar.
Ma'aunin tattalin arzikin (GDP) na kasar Sin ya karu da kashi 6.7 bisa 100 a farkon watanni ukun farkon shekarar 2018, idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, har ma ya dara hasashen da gwamnatin kasar ta yi na samun karuwar tattalin arzikin kasar da kashi 6.5 bisa 100.
Sheng ya kara da cewa, matsayin karuwar samar da kudade na M2, ana hasashen zai iya ribanyawa a shekarar ta 2019, yayin da za'a samu dagawar darajar yanayin zuba jari, haka zalika akwai yiwuwar samun sauye-sauye a tsarin masana'atun kasar, da kuma karuwar bukatun da ake dashi na ayyukan bada hidima. (Ahmad Fagam)