Mr. Song Xianmao ya bayyana cewa, tun daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban bana, yawan kayayyakin da aka yi shigi da ficinsu a kasar Sin zai kai dalar Amurka biliyan dubu 4.24, wato zai karu da 14.8% bisa na shekarar 2017. Daga cikinsu, yawan kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan dubu 1.91, wato ya karu da 18.4% bisa na shekarar bara. Sakamakon haka, an yi hasashen cewa, wannan adadi zai wuce dalar Amurka biliyan dubu 2. Mr. Song Xianmao ya nanata cewa, dalilin da ya sa aka samu wannan kyakkyawan sakamako shi ne saboda kasar Sin ta aiwatar da manufar shigo da karin kayayyaki daga sauran yankunan duniya.
Mr. Song ya nuna cewa, a shekara mai kamawa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar rage harajin kwastam da ake bugawa kan kayayyakin da ake shigo da su daga ketare, sannan za ta kara kyautata aikin kwastam ga kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin. (Sanusi Chen)