Cikin taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arzikin Sin na shekarar 2019 da aka yi a birnin New York na kasar Amurka a ranar 10 ga wata, Lin Yifu ya bayyana cewa, bayan kasar Sin ta fara aiwatar da matakan yin kwaskwarima a fannin tattalin arziki, wadanda suka hada da rage kayayyakin da aka samar fiye da kima, da rage yawan kayayyakin da aka adana da dai sauransu, Sin ta fara mai da hankali kan rage kudaden gudanarwar ayyukan kamfanoni da kuma kawar da matsin lambar da aka yiwa kamfanonin kasar wajen gudanar da ayyukansu, lamarin da zai taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin Sin. haka kuma, ya ce, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka kwanan baya, kamar su, rage harajin kamfanoni, kara saukin neman iznin gudanarwar ayyuka da dai sauransu, zasu ba da gudummawa wajen kafa yanayi mai kyau wajen gudanar da harkokin kasuwanci. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta samarwa kamfanonin ketare karin damammaki wajen zuba jari a kasar Sin ta hanyar inganta ayyukan gina yankunan ciniki cikin 'yanci a kasar. (Maryam)