Gudun jiragen kasa masu saurin gaske na Sin zai kai kilomita dubu 29
Jiya Talata, an fara amfani da hanyar jiragen kasa masu saurin gaske dake tsakanin birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da birnin Huangshan na lardin Anhui. Kuma bisa labarin da aka samu, an ce, cikin mako guda mai zuwa, kasar Sin za ta bude sabbin hanyoyin jiragen kasa masu saurin gaske guda 10, kana, adadin karuwar gudun jiragen kasa masu saurin gaske zai kai kilomita 2500, yayin da gudun jiragen kasa masu sauri gaske na kasar Sin baki daya zai kai kilomita dubu 29. Lamarin da ya kasance babban ci gaba da Sin ta cimma kan wannan aiki a shekarar 2018.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku