Sin: Kamata ya yi Amurka ta yi bayani kan sayen na'urorin leken asiri da ofisoshin jakadancinta dake kasashen waje
A ranar 21 ga wata, yanar gizo ta Wikileaks ta bayar da wasu takardu, inda aka nuna cewa, ofisoshin jakadancin kasar Amurka a kasashe da dama sun taba sayen na'urorin leken asiri. Game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya Litinin cewa, har yanzu kasar Amurka ba ta ba da amsa ba kan batun leken asiri na PRISM da kasar ta yi a shekaru biyar da suka gabata, amma yanzu yanar gizo ta Wikileaks ta kara bayar da wannan sabon labari, kamata ya yi kasar Amurka ta yi bayani sosai ga kasashen duniya.
Game da tambayoyin da aka yi mata kan lamarin, Madam Hua ta ba da amsa cewa, me ya sa ofisoshin jakadancin kasar Amurka dake kasashen waje suka sayi na'urorin leken asiri da yawa? Kuma su wane ne suke yin amfani da na'urorin? Mene ne burinsu? A 'yan kwanakin baya, kasar Amurka da wasu kawayenta sun yi zargi kan kasar Sin na wai ta lahanta tsaron yanar gizo ta Amurka. Wadannan takardun da Wikileaks ta bayar sun nuna cewa, kasar Amurka ta kara tsara wani wasan kwaikwayo ne irin na "barawo ne yake ihun barawo domin kokarin da yake yi na neman tsira". (Bilkisu)