A fannin kudin tafiyar da ayyukan yau da kullum na MDD, kudin da kasar Sin za ta bayar, a karon farko ya zarta na kasar Japan, inda kasar ta Sin ta zama kasa ta biyu a fannin yawan baiwa MDD kudi.
An ce, kudin da kasar Sin za ta samarwa MDD don tallafawa ayyukanta na yau da kullum ya karu daga kashi 7.92%, zuwa kimanin kashi 12%, na daukacin kudin da majalisar ke bukata a wannan fanni. Sa'an nan a fannin aikin wanzar da zaman lafiya, kudin da kasar Sin ta bayar ya karu daga kashi 10.24% zuwa kashi 15.22%, wanda shi ma ya kasance na biyu cikin kudin da kasashe dabam daban ke baiwa majalisar. (Bello Wang)