A yau Litinin, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wani rahoto kan nasarorin da aka samu, a fannin gudanar da aikin dasa bishiyoyi a arewacin kasar Sin cikin shekaru 40 da suka wuce.
Wajen taron gabatar da rahoton, mataimakin shugaban hukuma mai kula da bishiyoyi da tsirrai ta kasar Sin Liu Dongsheng, ya ce karin filin itatuwa da kasar Sin ta samu bisa aikin dasa bishiyoyin, ya riga ya kai kadada 30,143,000.
An fara aiwatar da aikin dasa bishiyoyi a arewacin kasar Sin ne a shekarar 1978, aikin da zai kammala a shekarar 2050, wanda zai shafi dasa bishiyoyi a filayen da fadinsu za su kai muraba'in kilomita 4,069,000, kwatankwacin kashi 42.4% na fadin kasar Sin. (Bello Wang)