Rahoton wanda Tarayyar Afrika AU da hadin gwiwar hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika na MDD da shirin raya kasashe na MDD suka hada, ya yi nazari kan kokarin inganta kula da sarrafa albarkatun nahiyar, musamman bukatar karfafa cibiyoyin lura da su da tsarukan inganta samun kudin shiga.
Rahoton kan muradun ci gaba masu dorewa na Arika na 2018, wanda aka gabatar yayin taro kan tattalin arzikin Afrika dake gudana a Kigali babban birnin Rwanda, ya ce bangaren albarkatun wata dama ce ta neman ci gaba ga nahiyar Afrika, baya ga damar samar da kudin gudanar da ayyukan ci gaba, amma kuma yana cike da kalubalen dake bukatar dukkan masu ruwa da tsaki da gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu da kungiyoyin al'umma da su yi kokarin sauya tsarin lura da albarkatun. (Fa'iza Msuatpha)