Mr. Negatu ya yi wannan tsokaci ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Litinin, a gefen taron karawa juna sani game da tattalin arzikin Afirka da aka bude a jiya a birnin Kigalin kasar Rwanda.
Ya ce jarin da sassa masu zaman kansu ke zubawa a nahiyar, musamman a bangaren sufuri da makamashi, da raya masana'antu, zai taimakawa nahiyar wajen gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin samar da yankin ciniki cikin 'yanci.
Taron na shekara shekara karo na 13, na da taken "hade sassan shiyyar Afirka da sauran nahiyoyin duniya domin ci gaban Afirka", kuma shirin MDD na samar da ci gaba, da hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD ne suka dauki nauyin gudanar da shi. Zai kuma gudana ne tsakanin ranekun Litinin zuwa Laraba, inda ake fatan ci gaba da nazarin dabarun gaggauta samar da karin ababen more rayuwa, da hade sassan shiyyar, da kau da duk wani tarnaki dake dakile zirga zirgar jama'a, da kayayyaki, da ayyukan hidimomi tsakanin iyakokin nahiyar ta Afirka. (Saminu Hassan)