in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru na nazarin sabbin hanyoyin samar da kudaden bunkasa ababen more rayuwa a Afirka
2018-12-04 10:16:52 cri
Kwararru da masana dake halartar taron karawa juna sani a fannin raya tattalin arzikin nahiyar Afirka, wanda ke gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda, na ci gaba da tattaunawa game da bukatar zakulo sabbin hanyoyin samar da kudade, domin bunkasa ababen more rayuwa a Afirka.

Da take tsokaci game da hakan, darakta a fannin tsare tsare, bincike da hasashen yanayin ci gaba ta bankin raya Afirka na AfDB Hanan Morsy, ta ce akwai bukatar bankado hanyoyin samar da kudade da za a yi amfani da su, wajen zurfafa ayyukan more rayuwa, matakin da tamkar aza tubali ne na bunkasa hadewar nahiyar wuri guda. Uwargida Hanan ta kara da cewa, matakin samar da sabbin dabarun samar da isassun kudade, da rage gibin karancin ababen more rayuwar jama'a a Afirka, zai taimaka wajen aiwatar da yarjejejiyar gudanar da cinikayya cikin 'yanci ta AfCFTA.

Shi kuwa a nasa bangaren, mataimakin babban sakataren kungiyar raya kasuwannin bai daya na yankunan gabashi da kudancin Afirka ko COMESA a takaice Kipyego Cheluget, cewa ya yi bukatun raya ababen more rayuwa na Afirka suna da matukar muhimmanci, sun kuma zartas da maganar samun tallafi daga kasa da kasa. Ya ce ana bukatar rancen makudan kudaden gudanarwa daga bankunan shiyyoyi da na kasa da kasa, domin cimma wannan buri.

Mahalarta taron dai na ganin karancin isassun ababen more rayuwa a nahiyar Afirka, na taka muhimmiyar rawa wajen fadada kalubalen hadewar nahiyar wuri guda. Sassan da nahiyar Afirka ta fi fuskantar cikas sun hada da rashin isassun titunan mota, da tasoshin jiragen ruwa, da layin dogo, wanda hakan ke tsauwala hada hadar sufuri da cinikayya a sassan nahiyar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China