Da yake jawabi a lokacin taron dandalin Afrika game da zuba jari a Johannesburg, shugaban bankin na AfDB ya ce, duk da irin dimbin kalubalolin da ake fuskanta a nahiyar, amma duk da haka nahiyar Afrika tana da abubuwa masu tarin yawa da za ta gabatarwa masu sha'awar zuba jari. "Afrika tana da albarkatu masu dimbin yawa, ma'adanai, mai da aikin gona. Muna son mu fito da abubuwan da Afrika ke da su. Mu a matsayinmu na cibiyar gudanar da harkokin kudi muna goyon bayan Afrika a matsayin wani muhimmin wajen zuba jari," in ji shi.
Biyar daga cikin 10 na wuraren da aka fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya yana nan a Afrika, in ji Adesina.
"Zuba jari a Afrika. Za mu iya zama wata babbar kasuwa. Muna son za mu samar da muhimman kayayyakin more rayuwa. Muna son ci gaban Afrika cikin sauri," in ji shi.
Adesina ya bayyana cewa sauye sauye da suka hada da dokokin gudanar da ayyuka, da sauya fasalin tsare tsare wajen aiwatar da ayyuka masu yawa a kasashen Afrika a shekaru masu yawa da suka gabata za su samar da kyakkyawan muhallin yin cinkayya a nahiyar Afrika.
Adesina ya yi amanna cewa, taron dandalin zuba jarin da ake gudanarwa za'a yi amfani da shi wajen tsara dabarun zuba jari na dogon lokaci wanda zai taimakawa bunkasuwar Afrika.
Ana sa ran za'a sanar da kulla yarjejeniyoyi na ayyukan biliyoyin dalolli a lokacin dandalin. (Ahmad Fagam)