Ana dai gudanar da taron mai lakabin "Sauyin da kimiya ta kawo a bangaren tattara haraji" ne karkashin inuwar dandalin ATAF. Yayin taron na yini 5 da aka bude jiya Litinin a kasar Uganda, mahalartansa za su nazarci yadda Uganda ta cimma nasarar hade sashen kimiyyarta da harkar tattara haraji.
Da take tsokaci game da taron, daraktar dandalin ATAF ta kasar Uganda Mary Baine, ta ce hade sassan kimiyya da fasaha da bangaren tattara haraji, na iya zama wata gagarumar dama a fannin inganta tsarin karbar haraji a Afirka, kana hakan zai baiwa nahiyar damar samun sabbin hanyoyi na kara yawan harajin da take samu.
Baine ta ce sabon salon zai taimakawa Afirka, wayen yaki da zurarewar kudade ta barauniyar hanya, wanda hakan ke sanya kasashen ta asarar kudade, da yawansu ya kai sama da dalar Amurka biliyan 50 a duk shakera.
Masana na cewa bin salon amfani da kimiyya wajen tattara haraji, na iya baiwa ma'aikatan sashen damar hada managarcin lissafi, ta yadda cikin sauki za a iya dora harajin da ya dace kan ko wane nau'in hajoji bisa cancanta. (Saminu Hassan)