Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afrika ECA, ta jadadda cewa, manyan sakamakon da aka samu yayin taron makon shirin raya ababen more rayuwa a Afrika (PIDA), wanda aka kammala a baya bayan nan, ya haifar da sabon kwarin gwiwar sauya salon samar da ababen more rayuwa a Afrika.
Hukumar ECA, ta bayyana haka ne yayin da makon shirin PIDA, wanda aka fara daga ranar Litinin zuwa Laraba a garin Victoria Falls na Zimbabwe ke kammaluwa, inda aka yi kira da hada hannu wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa dake hada kasashe daban-daban a fadin nahiyar, ta yadda za a samu dunkulewar tattalin arzikinta domin moriyar al'ummarta.
ECA ta kuma yabawa sakamakon karshe da aka samu yayin taron, inda mahalarta suka amince da ci gaba da kokarin gaggauta raya muhimman ayyukan more rayuwa a nahiyar.
Ta ce ayyukan shirin PIDA musammam ayyukan more rayuwa dake hada kasashe daban-daban, za su bunkasa dunkulewar nahiyar, kana ayyuka ne da ake bukata wajen bayyana damar da nahiyar ke da ita na samun ci gaba.
Masana da masu tsara manufofi da suka halarci taron sun yi kira ga dukkan kasashen Afrika, su kara inganta ayyakan da ake gudanarwa daga kaso 32 da suke kai yanzu, zuwa kaso 50, idan har ana son nahiyar ta cimma burinta na samun ci gaba. (Fa'iza Mustapha)