Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS, da Tarayyar Afrika AU da kuma MDD, sun bukaci kasar Guinea–Bissau ta gudanar da zabukan 'yan majalisar dokokin kasar a kan lokaci kuma bisa adalci da gaskiya.
Cikin wata sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa, hukumomin uku sun bukaci masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen tabbatar da samar da yanayin da ake bukata don tabbatar da gudanar da zabukan lami lafiya.
Kasar dake yankin yammacin Afrika, ta shirya gudanar da zabukan 'yan majalisar dokokin kasar ne ranar 18 ga watan Nuwamban dake tafe, sai dai ana maganar jinkirta zabukan domin karawa masu kada kuri'a lokacin rajista.
Hukumomin sun kuma yi kira ga kasashen Afrika da sauran kasashen waje, su hada hannu wajen samar da kayayyakin da ake bukata na gudanar da zabukan.
Sanarwar ta kara da cewa, zaben zai zama kari kan nasarorin da kasar ta samu, a don haka, aka fi bukatar goyon bayan al'ummomin kasashen waje fiye da ko yaushe. (Fa'iza Mustapha)