Jakadan Sin din ya yi wannan furuci ne bayan wata ganawa tare da sakataren kasa dake kula dangantaka, Augusto Poquena.
Bangarorin biyu sun bayyana burinsu na moriyar juna wajen yin aiki tare domin tabbatar da wani ci gaba mafi albarka ga al'ummomin kasashen biyu, in ji mista Wang.
A cewar jakadan Sin, kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa Guinee-Bissau.
Kasar Sin, na daya daga cikin muhimman kasashen abokan huldar ci gaba na kasar Guinee-Bissau, kuma mai taimakawa bangarorin noma da ababen more rayuwa sosai, in ji mista Wang.
Baya bayan nan, gwamnatin Sin ta baiwa Guinee-Bissau kayayyaki na darajar dalar Amurka miliyan 1,25 domin taimaka kasar kara bunkasa nomanta na shinkafa.
A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan aiki da gine gine, Malam Banjai, ya tabbatar da cewa Sin babbar abokiyar huldar dangantaka ce ta kasar Guinee-Bissau, don haka akwai bukatar a mai da hankali na musamman. (Maman Ada)