A cewar wata sanarwar cibiyar kungiyar ECOWAS dake Guinee-Bissau, madam Sirleaf za ta yi tattaunawa tare da takwaranta na Guinee Bissau, Jose Mario Vaz, da sauran bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Conakry da kuma wakilan gamayyar kasa da kasa.
Babban jigon takadama domin fita daga rikicin shi ne na zabin wani faraminista, a cewar yarjejeniyar Conakry, da aka rattaba wa hannu a karkashin jagorancin shugaban Guinee-Conakry Alpha Conde, za a dora ma nauyin kafa wata gwamnatin hadaka.
Masu ruwa da tsakin da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya na cigaba da aiwatar da ita bisa yadda suke so, musamman ma jam'iyyar PAIGC, wacce ta lashe zaben 'yan majalisun baya bayan nan da kujeru 57 da kuma jam'iyyar PRS, ta biyu a fagen siyasar Guinee Bissau da take rike da kujeru 41 a zauren majalisar dokokin kasar. (Maman Ada)