Shugaban kasar Guinea Bissau José Mário Vaz, ya sanar a jiya Litinin 16 ga wata cewa, ya nada Aristides Gomes a matsayin sabon firaiministan kasar.
Umurnin ya nuna cewa, babban aikin Aristides Gomes shi ne kafa sabuwar gwamnati domin share fagen zaben majalisa.
An bada labarin cewa, Gomes wanda babban jami'i ne na jam'iyyar PAIGC, ya taba rike wannan matsayi daga watan Nuwambar shekarar 2005 zuwa watan Afrilu na shekarar 2007.
Tun daga watan Agusta na shekarar 2015, bangarori daban-daban a kasar Guinea Bissau suke fuskantar bambancin ra'ayi a tsakaninsu game da nadin dan takarar firaministan, abin da ya haddasa rikicin siyasa a kasar. jam'iyyar PAIGC wadda take fi rinjaye cikin majalisar dokokin kasar bata amince da dan takarar da Vaz ya nada ba, a ganinsu nada wani dan takara a matsayin firaminista ba tare da samun amincewar jam'iyyarsu ba ya sabawa tsarin mulkin kasar.
Sai kuma a watan Oktomban shekarar 2016, shugabannin jam'iyyu daban-daban na kasar da wakilan al'umma da kungiyoyin addinai su ma sun yi tattaunawa a Conakry hedkwatar kasar tare da sanya hannu kan wata yarjejeniya. Bisa abubuwan da aka tanada cikin wannan yarjejeniyar, kamata yayi dan takarar firaminista ya samu amincewa daga jam'iyyu daban-daban na kasar, ta yadda za a kafa sabuwar gwamnati cikin lumana. (Amina Xu)