Jose Viegas Filho, wakilin musamman na babban sakataren MDD a Guinea-Bissau, kana shugaban ofishin tabbatar da zaman lafiya na MDD dake kasar Guinea-Bissau (UNIOGBIS), ya bukaci a samu cikakken goyon bayan kasa da kasa don taimakawa kasar ta yammacin Afrika.
Filho ya bayyanawa MDDr wasu daga cikin wahalhalun da suke fama da su wajen shirye-shiryen gudanar da zaben majalisar dokokin wanda aka tsara gudanarwa a ranar 18 ga watan Nuwamba, daga cikin matsalolin akwai rashin amincewar da wasu masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasar kasar ke nunawa game da ware kwanaki 30 da gwamnatin kasar a matsayin lokacin yin rejistar masu zabe, yayin da dokar kasar ta amince da kwanaki 90 don yin rejistar, da kuma jinkirin da ake samu na rashin isar na'urorin tattara bayanai a kan lokaci.
A hannu guda kuma, babban jami'in MDD ya kuma bayyana irin ci gaban da aka samu, wadanda suka hada da aiwatar da dokar sabon tsarin kawar da banbancin jinsi tun a ranar 2 ga watan Agusta, wanda aka baiwa matan kasar kashi 36 bisa 100 na guraben wakilci don neman tsayawa takara a majalisar dokokin kasar da sauran guraben shugabanci a zabukan kananan hukumomin kasar, har da manyan mukamai da za'a nada a kasar. (Ahmad Fagam)