Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhun MDD ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Guinea Bissau da su maida hankali ga muradun jama'a, da maido da zaman lafiya a fannin siyasar kasar, tare da warware rikicin siyasa cikin hanzari. Kana ya nuna damuwa ga batutuwan da suka shafi aikata manyan laifufuka a tsakanin kasashen duniya da masu tsattsauran ra'ayi, barazanar ta'addancin da kasar ke fuskanta.
A watan Agustan shekarar 2015 ne, aka samu rashin jituwa tsakanin bangarori daban daban na kasar Guinea Bissau dangane da batun nada firaministan kasar, lamarin da ya haifar da rikicin siyasa a kasar. A watan Nuwanban shekarar 2016, shugaban kasar José Mário Vaz ya nada mai ba da shawara ga tsohon shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo a matsayin firaministan kasar, amma kungiyar 'yan adawa ta ki amincewa da nadin nasa. (Zainab)