Daga ranar 2 zuwa 3 ga wata, tawagar wakilan kasar Sin, karkashin jagoranci na mataimakin firaminista, kana jagoran shawarwarin tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Amurka na kasar Sin, Liu He, ya yi shawarwari da tawagar Amurka dake karkashin jagoranci na ministan harkokin kasuwancin kasar, game da batun tattalin arziki da cinikin tsakanin kasashen biyu.
Bangarorin biyu, sun yi musayar ra'ayi cikin yanani mai kyau, kan yadda za a aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma a birnin Washington, da kuma batutuwan dake shafar aikin gona da makamashi da dai sauransu, inda aka samu babban ci gaba ta fuskar wannan aiki, sai dai ana bukatar bangarorin biyu su tabbatar da bayanai filla-filla game da batun. (Maryam)