A yayin shawarwarin, kasashen biyu sun aika da tawagarsu dake kunshe da muhimman jami'ai. Sai dai a hakika an sha matukar wahala wajen shawarwarin, dukkannin bangarorin biyu sun fuskanci babban matsin lamba, saboda a yayin da suke bin hakikanin yanayin da ake ciki, sai dai a a sa'i guda akwai bukatar su cimma matsaya daya. Muddin ana fatan cimma wannan buri, dole ne su tabbatar cewa, su wanene ake yin wannan shawarwarin domin su, kuma su wanene suke ba da hidima gare su. Game da haka, bangaren Sin ya tsaya kan manufar gudanarwa ta Xi Jinping, shugaban koli na kasar, wato sanya jama'a su kara cin gajiya. Wannan ne ma ya samu amincewa daga wajen bangaren Amurka. A yayin da yake ganawa da manzon musamman na shugaba Xi Jinping, kuma jagora kan shawarwarin na bangaren Sin mista Liu He a ranar 17 ga wata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, yana fatan hadin kai a tsakanin kasashen biyu zai kara kawo moriya ga jama'ar kasashensu. Hakan kuma an gano cewa, jama'ar kasashen Sin da Amurka ne suke kasancewar masu cimma nasara a gun wannan shawarwarin dake jawo hankulan duk duniya.
Kasar Sin zata kara sayen kayayyakin ciniki da na hidima daga wajen Amurka, ciki har da kayayyakin aikin gona, mai, makamashi mai tsabta, da kuma kayayykin kimiyya da fasaha na zamani. Abubuwan dake cikin hadaddiyar sanarwa sun nuna manufar zaman daidai wa daida da samun moriyar juna, wanda a ko da yaushe kasar Sin ke bi, kuma sun nuna sahihancin kasashen biyu na mai da hadin kan tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu a matsayin jigo wajen inganta dangantakar dake tsakaninsu. (Bilkisu)