Yayin ganawarsu, Wang Yi ya ce, a yanzu haka yanayin da kasashen duniya ke ciki na da sarkakiya, saboda haka kokarin kiyaye hulda mai kyau tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci sosai. Don cimma wannan burin, matakan da za a dauka sun hada da:
Na farko, bari shugabannin kasashen 2 su tabbatar da manyan tsare-tsaren da za a yi amfani da su, wajen raya hulda tsakanin kasashen Sin da Amurka. Na biyu, a yi kokarin zurfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin 2, don tabbatar da tushen huldar dake tsakaninsu. Na uku, habaka hadin kan Sin da Amurka a fannin harkokin yankin da ake ciki da na kasa da kasa.
A nasa bangare, mista Mike Pompeo ya ce, a ganin kasar Amurka, huldar dake tsakaninta da kasar Sin, ba wai wani bangare daya ne ke samun riba ba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hassara. Saboda haka kasar na son yin kokari tare da kasar Sin, don kara kyautata huldar dake tsakaninsu. (Bello Wang)